Thursday, January 10, 2019

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTAR DA KANSA AKAN DAKATAR DA 'YAN MAJALISU HUDU DA AKAYI.

Daga Salisu Bello .

Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar dokokin Jihar Zamfara guda hudu da Majalisar tayi karkashin jagorancin Rt Hon Sanusi Garba Rikiji a satin da ya gabata.

Wannan ya biyo bayan ganawar sirri da yayi tare da Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma kuma Babban jigo a siyasar Zamfara wato Sanata Ahmad Sani Yarima a gidanshi dake Abuja.

Gwamnan ya kuma bukaci Sanata Yarima da ya kira wadannan 'yan Majalisu domin basu hakuri  akan abunda ya faru wanda anyi shi ne ba bisa ka ka'ida ko doka ba.

Rahotannin da muke samu a yau sun nuna wadannan 'yan Majalisun suna Babban Birnin tarayya wato Abuja domin ganawar sirri da shi Sanata Ahmad Sani Yarima.

Sunday, January 6, 2019

LABARI DA DUMI-DUMIN SHI.

LABARI DA DUMI-DUMIN SHI.

A kwanakin baya mun kawo maku labarin cewa, an dakatar da 'yan majalisa guda Hudu (4) a jihar Zamfara, wadanda suka hada da ...
Hon Abdullahi Muhammad Dansadau
Hon Mani Mummini Masamar Mudi
Hon Salisu Musa Kainuwa
Hon Mansur Ahmad Bungudu.

Hantsi ta tsinkawo maku wasu Karin 'yan majalisa Uku (3) da ake shirin sake dakatar wa  Bayan bakwai din da suka ware kansu a baya, Wanda yanzu yawan wadanda zasu rabu da sashen gwamnati yake dab da zama Goma (11) Cikin Ashirin da Hudu.

Wadanda ake shirin dakatarwar ana tuhumar su ne da Alaka da tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata a halin yanzu, Sanata Ahmad Rufa'i Sani, kasancewar ana tuhumar su da Cewa, sune idanun shi a majalisar.

Wadanda ake tuhumar sun hada da..
Hon. Hashimu M Shehu Gazura
Hon. Aminu Dan Jibga
Hon yusuf Moriki.

Hmmm, Bahaushe yace, Indai anbi daga-daga...

NAIRA MILIYAN 7 SUKA AMSA DON DAKATAR DA YAN MAJALISA HUDU (4).

Daga_
Abdulmuminu Sanusi.
Sanin kowane Mai bibiyar al'amuran siyasa ne Cewa, kwanakin nan jihar Zamfara ta fada cikin sabuwar dambarwar siyasa, Wadda har takai ga dakatar da 'yan majalisun Jihar su hudu wadan da ake zargi da laifukka da ba Suda tushe balle makama.

Bayan dogon bincike da jaridar Hantsi ta aiwatar mun gano ababen da aka nunke a cikin wannan badakalar ta dakatar da su.
Wani sashe na 'yan majalisun masu goyon Bayan gwamnatin sune Akaba zunzurutun Kudi har naira miliyan bakwai, ta hannun Mai tsawatar wa a majalisar Hon. Isah Abdulmuminu talatar Mafara.
Kuma Ko wane Dai daga cikin su, ya samu Naira Duhu Dari Uku da goma (310).
Duka wadannan ababe anyi sune sharar fage ga Kudirin dake akwai Kasa, na tsige mataimakin gwamnan Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala Liman.
Saboda sunaso su Samar da Rinjaye Mai karfi a lokacin Gudanar da aikin tsige mataimakin gwamnan na Zamfara.
Allah ya kyauta.


Saturday, January 5, 2019

IDAN YARI BAI IYAWA, YA SAUKA_ INJI ATIKU

Dan Takarar shugaban Kasa a inuwar Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya soki kiran da gwamnan jihar Zamfara ya ke yi na a saka dokar ta baci a jihar saboda rashin tsaro da ake fama da shi.
Idan ba a manta ba ko a yau Alhamis gwamnan jihar Zamfara Yari ya bayyana wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa idan har saka dokar ta baci shine zai samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara a shirye yake da yayi murabus.
Sai dai kuma, kamar yadda yake ganin hakan ne kila mafita ga tsaron jihar, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya fadi cewa sam basu tare a wannan shawara da yake badawa.
A takarda da Pharank Shuaibu ya fitar a madadin Atiku, ya ce wannan shiri ne kawai don a muzguna wa ‘Yan siyasa.
” Idan gwamnan jihar Yari ba zai iya ba kaucewa zai yi ya ba da wuri amma ba wai ya rika kira da a saka dokar ko ta baci a jihar ba. Yin haka sabawa doka ce da kuma muzguna wa mutane. Ana neman yadda za a takura wa mutane ne kawai a hana su walwala saboda son zuciya da kuma dagewa da Buhari yayi na sai dole-dole ya zarce ko da karfin tsiya ne.
Atiku ya kara da cewa muddun aka yi haka za a saka shingaye a tituna da wurare da dama a jihar da hakan zai takura wa walwalar mutane.

Friday, January 4, 2019

'YAN MAJALISAR JIHAR ZAMFARA, SHIN KO GWAMNA A A YARI YA GYARA NE?


Maganar gaskiya jihar zamfara muna da yan majalisun jaha da basusan me ya kamata ba. Na saurari jagoran majalisar dokoki ta jahar Zamfara yana cewa, "Duk da yake Munje hutu kuma ba zamu dawo bakin aiki ba sai 15 ga watan Janairu na wannan shekara, mun Kira zaman gaugawa ne domin la'akari da muhimmancin da ke akwai ga bukatar da Gwamna ya ya gabatar mu na, ta karin Wa'adin watanni hudu ga shuwagabannin kananan hukumomi na jaha."

Abun ban haushi da takaici anan shine, duk kashe-kashen nan da akeyi a fadin jahar zamfara, ba suga muhinmancin janye hutunsu su dawo domin janyo hankalin gwamnati da tayi abunda ya dace domin tsare rayukan al'ummar da suke wakilta ba, amma suna iya dawowa akan matsalar ciyamoma.

Wallahi! Al'ummar Zamfara mudawo cikin hayyacin mu zabi wakillai na gari ba irin wadannan jeka na yika  ba, wadanda suka dauki samun su da rashin su suka ta'alla kashi ga wani  mai mulki.

Ku dubi yadda a jihar Zamfara yadda gwamna ya wulakanta majalisa, ya maidasu tamkar wani bangare na majalisar zartawwa.

Shi kakakin majalisar Sunusi Rikiji ya zamto tamkar jeka na yika, bayan Al'ummar mazabar Gusau ta daya suka tura shi don wakilce su, ya maida Gwamna tamkar wani dodo, duk da shi ne ya taba fada a kafofin yada labarai na gida da na waje cewa " gwamna Abdul'aziz yari ya cika dukkan sharuddan tsigewa daga karagar mulki".
Shin abin tambaya a nan, Shi Gwamnan ya gyara ne, don al'ummar Zamfara na cikin duhu, saboda maganar tabi shanun talla.

Yan majalisar jahar Zamfara sun watsar da damar da kundin tsarin mulki ya basu, sun jefa al'ummar jahar Zamfara cikin halin kunci, domin sun kasa aiwatar da ayukkan da Al'umma suka zabo su domin aiwatar ma su!

Wai kamar yadda ma su iya magana kance,: "Kukan kurciya jawabi ne amma fa ga mai hankali".

SHIRE-SHIREN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA SUN KANKAMA.

Daga...
Aliyu Sani Gusau.

Dakatar da yan Majalisu 7 hadi da cewa sun karbi Naira miliyan (30m) ga wani Dan takarar Gwamnan jihar zamfara, bai rasa Nasaba da shire-shiren da ke akwai na tsige mataimakin gwamnan Zamfara Malam Ibrahim wakkala liman...
------------------------------------------------

1. Hon. Salisu Musa kainuwa Tsafe,
2. Hon. Abdullahi Mai Kano Dan sadau,
3. Hon. Dayyabu Rijiya,
4. Hon. Mansur Ahmed Bungudu,
5. Hon. Mani malam  Muminu,
6. Hon. Hashimu Gazura,
7. Hon. Abubakar Ajiya Bukuyum,

Wadannan yan majalisun Sune suka Kira taron manema labarai yau Jumu'ah a Gusau babban birnin jihar zamfara, domin bayyanawa duniya katobarar da Majalisar dokoki tayyi, karkashin jagoranci kakakin majalisar dokokin jihar zamfara da kuma bandar dake akwai kwance Kasa Na Dakatar da wasu daga cikin yan majalisar dokokin da akayi ba akan ka'ida ba,

Wayanda aka Dakatar sun hada da,

1. Hon. Salisu Musa Tsafe,
2. Hon. Mansur Bungudu,
3. Hon. Abdullahi Dan sadau,
4. Mani malam Muminu,

Mai magana a madadinsu lokacin taron Hon. Salisu kainuwa yace an dakatar dasu ne kawai akan kin amincewa da korafin Gwamna yari, akan Karin wa'adin daya nemawa shugabanin kananan hukumomi Wanda suka fadawa majalisa cewa wannan bukata ta sabawa doka.

Sannan ya Kara da cewa an dakatar dasu ne a lokacin Hutu Wanda majalisa keyi.

Kuma Babu wani kwamiti da aka kafa musu kafin dakatar dasu daga majalisar  balle su Kare kansu anyi haka ne kawai don dalilin siyasa saboda Sunce abi doka Wanda kuma shine aikin Dan majalisa.

Sanan yakara dacewa dakatar damu tabbas banan abun zai tsayawaba, saboda wannan na nuni da tsohon shirin su na cire mataimakin gwamnan Zamfara.

LABARI DA DUMI-DUMI


Yan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar suna taro da manema labarai domin fitar da matsayar su akan dakatarwa  da kuma  karin wa'adi da gwamnatin jihar Zamfara tayi wa Chiyamoman kananan  Hukumomi.

Zamu kawo maku sauran bayani  nan gaba kadan.

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTAR DA KANSA AKAN DAKATAR DA 'YAN MAJALISU HUDU DA AKAYI.

Daga Salisu Bello . Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar do...