Thursday, January 10, 2019

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTAR DA KANSA AKAN DAKATAR DA 'YAN MAJALISU HUDU DA AKAYI.

Daga Salisu Bello .

Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar dokokin Jihar Zamfara guda hudu da Majalisar tayi karkashin jagorancin Rt Hon Sanusi Garba Rikiji a satin da ya gabata.

Wannan ya biyo bayan ganawar sirri da yayi tare da Sanata mai wakiltar Zamfara ta yamma kuma Babban jigo a siyasar Zamfara wato Sanata Ahmad Sani Yarima a gidanshi dake Abuja.

Gwamnan ya kuma bukaci Sanata Yarima da ya kira wadannan 'yan Majalisu domin basu hakuri  akan abunda ya faru wanda anyi shi ne ba bisa ka ka'ida ko doka ba.

Rahotannin da muke samu a yau sun nuna wadannan 'yan Majalisun suna Babban Birnin tarayya wato Abuja domin ganawar sirri da shi Sanata Ahmad Sani Yarima.

Sunday, January 6, 2019

LABARI DA DUMI-DUMIN SHI.

LABARI DA DUMI-DUMIN SHI.

A kwanakin baya mun kawo maku labarin cewa, an dakatar da 'yan majalisa guda Hudu (4) a jihar Zamfara, wadanda suka hada da ...
Hon Abdullahi Muhammad Dansadau
Hon Mani Mummini Masamar Mudi
Hon Salisu Musa Kainuwa
Hon Mansur Ahmad Bungudu.

Hantsi ta tsinkawo maku wasu Karin 'yan majalisa Uku (3) da ake shirin sake dakatar wa  Bayan bakwai din da suka ware kansu a baya, Wanda yanzu yawan wadanda zasu rabu da sashen gwamnati yake dab da zama Goma (11) Cikin Ashirin da Hudu.

Wadanda ake shirin dakatarwar ana tuhumar su ne da Alaka da tsohon gwamnan jihar Zamfara kuma Sanata a halin yanzu, Sanata Ahmad Rufa'i Sani, kasancewar ana tuhumar su da Cewa, sune idanun shi a majalisar.

Wadanda ake tuhumar sun hada da..
Hon. Hashimu M Shehu Gazura
Hon. Aminu Dan Jibga
Hon yusuf Moriki.

Hmmm, Bahaushe yace, Indai anbi daga-daga...

NAIRA MILIYAN 7 SUKA AMSA DON DAKATAR DA YAN MAJALISA HUDU (4).

Daga_
Abdulmuminu Sanusi.
Sanin kowane Mai bibiyar al'amuran siyasa ne Cewa, kwanakin nan jihar Zamfara ta fada cikin sabuwar dambarwar siyasa, Wadda har takai ga dakatar da 'yan majalisun Jihar su hudu wadan da ake zargi da laifukka da ba Suda tushe balle makama.

Bayan dogon bincike da jaridar Hantsi ta aiwatar mun gano ababen da aka nunke a cikin wannan badakalar ta dakatar da su.
Wani sashe na 'yan majalisun masu goyon Bayan gwamnatin sune Akaba zunzurutun Kudi har naira miliyan bakwai, ta hannun Mai tsawatar wa a majalisar Hon. Isah Abdulmuminu talatar Mafara.
Kuma Ko wane Dai daga cikin su, ya samu Naira Duhu Dari Uku da goma (310).
Duka wadannan ababe anyi sune sharar fage ga Kudirin dake akwai Kasa, na tsige mataimakin gwamnan Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala Liman.
Saboda sunaso su Samar da Rinjaye Mai karfi a lokacin Gudanar da aikin tsige mataimakin gwamnan na Zamfara.
Allah ya kyauta.


Saturday, January 5, 2019

IDAN YARI BAI IYAWA, YA SAUKA_ INJI ATIKU

Dan Takarar shugaban Kasa a inuwar Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya soki kiran da gwamnan jihar Zamfara ya ke yi na a saka dokar ta baci a jihar saboda rashin tsaro da ake fama da shi.
Idan ba a manta ba ko a yau Alhamis gwamnan jihar Zamfara Yari ya bayyana wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa idan har saka dokar ta baci shine zai samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara a shirye yake da yayi murabus.
Sai dai kuma, kamar yadda yake ganin hakan ne kila mafita ga tsaron jihar, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya fadi cewa sam basu tare a wannan shawara da yake badawa.
A takarda da Pharank Shuaibu ya fitar a madadin Atiku, ya ce wannan shiri ne kawai don a muzguna wa ‘Yan siyasa.
” Idan gwamnan jihar Yari ba zai iya ba kaucewa zai yi ya ba da wuri amma ba wai ya rika kira da a saka dokar ko ta baci a jihar ba. Yin haka sabawa doka ce da kuma muzguna wa mutane. Ana neman yadda za a takura wa mutane ne kawai a hana su walwala saboda son zuciya da kuma dagewa da Buhari yayi na sai dole-dole ya zarce ko da karfin tsiya ne.
Atiku ya kara da cewa muddun aka yi haka za a saka shingaye a tituna da wurare da dama a jihar da hakan zai takura wa walwalar mutane.

Friday, January 4, 2019

'YAN MAJALISAR JIHAR ZAMFARA, SHIN KO GWAMNA A A YARI YA GYARA NE?


Maganar gaskiya jihar zamfara muna da yan majalisun jaha da basusan me ya kamata ba. Na saurari jagoran majalisar dokoki ta jahar Zamfara yana cewa, "Duk da yake Munje hutu kuma ba zamu dawo bakin aiki ba sai 15 ga watan Janairu na wannan shekara, mun Kira zaman gaugawa ne domin la'akari da muhimmancin da ke akwai ga bukatar da Gwamna ya ya gabatar mu na, ta karin Wa'adin watanni hudu ga shuwagabannin kananan hukumomi na jaha."

Abun ban haushi da takaici anan shine, duk kashe-kashen nan da akeyi a fadin jahar zamfara, ba suga muhinmancin janye hutunsu su dawo domin janyo hankalin gwamnati da tayi abunda ya dace domin tsare rayukan al'ummar da suke wakilta ba, amma suna iya dawowa akan matsalar ciyamoma.

Wallahi! Al'ummar Zamfara mudawo cikin hayyacin mu zabi wakillai na gari ba irin wadannan jeka na yika  ba, wadanda suka dauki samun su da rashin su suka ta'alla kashi ga wani  mai mulki.

Ku dubi yadda a jihar Zamfara yadda gwamna ya wulakanta majalisa, ya maidasu tamkar wani bangare na majalisar zartawwa.

Shi kakakin majalisar Sunusi Rikiji ya zamto tamkar jeka na yika, bayan Al'ummar mazabar Gusau ta daya suka tura shi don wakilce su, ya maida Gwamna tamkar wani dodo, duk da shi ne ya taba fada a kafofin yada labarai na gida da na waje cewa " gwamna Abdul'aziz yari ya cika dukkan sharuddan tsigewa daga karagar mulki".
Shin abin tambaya a nan, Shi Gwamnan ya gyara ne, don al'ummar Zamfara na cikin duhu, saboda maganar tabi shanun talla.

Yan majalisar jahar Zamfara sun watsar da damar da kundin tsarin mulki ya basu, sun jefa al'ummar jahar Zamfara cikin halin kunci, domin sun kasa aiwatar da ayukkan da Al'umma suka zabo su domin aiwatar ma su!

Wai kamar yadda ma su iya magana kance,: "Kukan kurciya jawabi ne amma fa ga mai hankali".

SHIRE-SHIREN TSIGE MATAIMAKIN GWAMNAN ZAMFARA SUN KANKAMA.

Daga...
Aliyu Sani Gusau.

Dakatar da yan Majalisu 7 hadi da cewa sun karbi Naira miliyan (30m) ga wani Dan takarar Gwamnan jihar zamfara, bai rasa Nasaba da shire-shiren da ke akwai na tsige mataimakin gwamnan Zamfara Malam Ibrahim wakkala liman...
------------------------------------------------

1. Hon. Salisu Musa kainuwa Tsafe,
2. Hon. Abdullahi Mai Kano Dan sadau,
3. Hon. Dayyabu Rijiya,
4. Hon. Mansur Ahmed Bungudu,
5. Hon. Mani malam  Muminu,
6. Hon. Hashimu Gazura,
7. Hon. Abubakar Ajiya Bukuyum,

Wadannan yan majalisun Sune suka Kira taron manema labarai yau Jumu'ah a Gusau babban birnin jihar zamfara, domin bayyanawa duniya katobarar da Majalisar dokoki tayyi, karkashin jagoranci kakakin majalisar dokokin jihar zamfara da kuma bandar dake akwai kwance Kasa Na Dakatar da wasu daga cikin yan majalisar dokokin da akayi ba akan ka'ida ba,

Wayanda aka Dakatar sun hada da,

1. Hon. Salisu Musa Tsafe,
2. Hon. Mansur Bungudu,
3. Hon. Abdullahi Dan sadau,
4. Mani malam Muminu,

Mai magana a madadinsu lokacin taron Hon. Salisu kainuwa yace an dakatar dasu ne kawai akan kin amincewa da korafin Gwamna yari, akan Karin wa'adin daya nemawa shugabanin kananan hukumomi Wanda suka fadawa majalisa cewa wannan bukata ta sabawa doka.

Sannan ya Kara da cewa an dakatar dasu ne a lokacin Hutu Wanda majalisa keyi.

Kuma Babu wani kwamiti da aka kafa musu kafin dakatar dasu daga majalisar  balle su Kare kansu anyi haka ne kawai don dalilin siyasa saboda Sunce abi doka Wanda kuma shine aikin Dan majalisa.

Sanan yakara dacewa dakatar damu tabbas banan abun zai tsayawaba, saboda wannan na nuni da tsohon shirin su na cire mataimakin gwamnan Zamfara.

LABARI DA DUMI-DUMI


Yan majalisar dokokin jihar Zamfara da aka dakatar suna taro da manema labarai domin fitar da matsayar su akan dakatarwa  da kuma  karin wa'adi da gwamnatin jihar Zamfara tayi wa Chiyamoman kananan  Hukumomi.

Zamu kawo maku sauran bayani  nan gaba kadan.

Thursday, January 3, 2019

MAJALISAR DOKOKIN JIHAR ZAMFARA TA DAKATAR DA YAN MAJALISU GUDA HUDU (4) KAN GOYON BAYAN G8 DA SUKAI.


Daga Bello Ahmad Tsafe...

Majalisar dokokin jihar Zamfara a karkashin jogirancin Hon Rt Sanusi Garba Rikiji ta dakatar da 'Yan majalisar dokokin Jihar masu goyon bayan mataimakin Gwamnan Jihar har su Gudu (4).

A zaman ta na yau Alhamis 3/1/2019 wanda Shugaban majalisar ya jagoranta, Hon. Isah Abdulmumini T/Mafara ya gabatar da kuduri na dakatar da wadannan 'Yan majalisu guda gudu (4).

Yan Majalisun sun hada da Hon. Abdullahi Muhammed Dansadau wanda shine mai tsawatarwa na majalisar kuma mai wakiltar Maru ta Kudu, sai kuma Hon. Malam Mani Masaba, Hon. Mansur Ahmad Musa Bungudu Mai wakiltar Bungudu ta Yamma tare da Hon. Salisu Musa Tsafe Kainuwa Dan Majalisa  mai wakiltar Tsafe ta Gabas.

Bincike ya nuna cewa, dakatar da su bai rasa alaka da goyon bayan kugiyar nan ta G8 wadda tayi turjiya game da yunkurin Gwamnan jihar na dauki dora da  ya so yayi.

Wata majiya da muka samu kuma tace Shugabannin majalisar suna jin tsoron idan Gwamna ya kawo kasafin kudi na shekarar bana a majalisar wadannan Yan majalisar suna iya kin aminta da shi.

RAHOTON ZAMAN KOTU NA YAU ALHAMIS 3-1-2019


Daga... 
Ibrahim Bello Gusau Ibg

Abun da ake tsammani a zaman kotu na yau alhamis 3-1-2019 bai wuce na bayyanar shugabar hukumar zabe ta jahar zamfara, Dr. Asma'u Maikudi, ba amma hakan bai yuyu ba.

Jim kadan bayan shigowar mai shari'a, Justice Bello Muhammad Shinkafi, a zauren kotu, an fara gabatar da kai na lauyoyi daga kowane bangare kamar yadda aka al'adanta inda daga bisani anka gayyato dai daga cikin ma'aikatan wannan kotu mai suna Malam Bello da aka dora ma alhakin hannun ta sammace zuwa ga ita shugabar hukumar zabe ta jahar zamfara da yazo yayi ma kotu bayani inda aka kwana akan mika wannan sammace.

A cikin jawabin da yayi ma kotu, Malam Bello, ya bayyana cewa a lokacin da ya dauki wannan sammace zuwa ofishin ta, an hana shi ganin ta. Ya nemi sakatarin ta da ya hada shi da ita amma hakan bai yuyu ba.

Ya tambaye shi ina ta tafi, sai sakatarin yacce bai sani ba. Ya sake tambayar shi yaushe ake sa ran ta dawo, sai sakatarin yacce bai sani ba.

Ma'aikacin kotun, Malam Bello, ya dauki wannan sammace zuwa gidan ta domin hannun ta shi zuwa gare ta amma a cewar shi jami'an tsaron gidan na ta, sun ka hana shi ganin ta don haka wannan shi ne takaitaccen bayanin da zai yi ma kotu kuma yanzu haka ga sammacen a hannu shi.

SHARHI

Ga ka'ida ta kotu, idan irin haka ta faru, to abun da ake yi shi ne ; a lika sammacen a bakin ofishin wanda za a baiwa shi, ko a kofar gidan shi, ko kuma a buga shi a jarida sannan a ba da tsawon lokacin da ake sa ran zai ga sammacen. Idan kuma hakan ya chutura, sai kotu ta bada takardar izinin kamu  (Arrest Warrant) na a kamo shi a duk inda ya ke kuma idan haka ta faru, akwai dauri na tsawon wata shidda (6) a gidan yari.

-----------------------

Bayan da shi ma'aikacin wannan kotu ya kammala jawabi, sai lauyan Sanata Marafa, John shaka, ya miike tsaye inda ya gabatar da godiya da kuma yaba ma wannan kotu akan wadan nan matakan da ta dauka na ganin wannan sammace ya isa hannun Dr. Asama'u amma a cewar shi (Lauyan Marafa) la'akari da lokaci na ta tafiya, yana sanar da kotu cewa ya janye wannan bukatar ta gayyato ita wannan shugabar hukumar ta zabe kuma zai tsaya daga nan.

A dayan bangaren, lauyan uwar jam'iyyar APC ta kasa ya nemi kotu da ta ba shi dama domin gabatar da wasu takardu da ake sa ran martani ne (Counter Claim) ga wata bukata da lauyan Sanata Marafa ya shigar a kwanakkin baya inda shi lauyan Sanata Marafa yayi gyara da shari'ar shi cewa yana rokon kotu cewa idan ta hukunta cewa ba a yi zabe ba, a lokaci daya yana neman kotu da ta umurci uwar jam'iyyar APC da ta shirya sabon zaben fidda gwani a cikin kwana bakwai (7) kachal, wanda wannan gyaran ne lauyan bangaren uwar jam'iyya ke son maida martani (Counter claim) inda wannan bukatar ta shi (lauyan uwar jam'iyya) ta hadu da turjiya daga lauyan Sanata Marafa da kuma lauyan bangaren ma su shigar da kara (gwamnati) wanda daga nan ne mai shari'a ya dage zaman kotun inda anka je hotu har sai an dawo.

Bayan dawowa daga hutu na farko da na biyu, mai shari'a, Justice Bello Muhammad Shinkafi, ya aminta da waccan bukatar da lauyan bangaren uwar jam'iyya ya gabatar inda anka ba shi nan da zuwa gobe jumu'a 4-1-2019 da ya gabatar da abun da yake so ya gabatar.

Domin kauce ma cigaba da kawo rudani a cikin al'umma, lauyan Sanata Marafa, John shaka, ya nemi kotun da ta hana kowane irin lauya yin hira da yan jaridu bayan zaman kotu har sai an kammala shari'ar baki dayan ta domin a cewar shi, suna kawo rudani a cikin al'umma a dalilin irin bayanan da su ke baiwa yan jaridu kuma kotu ta aminta da hakan.

Daga karshe, an dage zaman kotun har sai zuwa gobe jumu'a 4-1-2018 idan mai rayuwa da kashewa ya kaimu.

Allah ya ci gaba da dora ma su gaskiya akan makaryata a kotu.


A SHIRYE NAKE DA INBAR OFISHINA _ AA YARI

Gwamnan Jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, ya ce yana shirye ya dakatar da ofishin idan wannan shine abin da ake bukata don mayar da zaman lafiya da tsaro ga jihar.
Jihar Zamfara dai Tana fama da yan fashi da makamai wadanda ke kashe Al'umma kuma suna sace su don kudin fansa.
An yi kira a kwanan nan don neman a kafa dokar tabaci ta musamman kamar yadda tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo ya kafa a Jihar Filato.
Bayan wannan furcin, gwamnan da mataimakinsa sun watsar da ofisoshin su na tsawon watanni shida. Wannan matsayi ya soki wasu a matsayin dan wasan kwaikwayon ko da yake ya mayar da zaman lafiya a Jihar Filato.
Mista Yari a makon da ya gabata ya ce yana goyon bayan Kafa dokar ta baci a jiharsa.
Da yake jawabi tare da wakilan majalisar dokokin kasar ranar Alhamis bayan ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari, Mista
Yari ya ce "Ba na siyasa ba ne, muna magana akan rayuwar dan Adam a nan. Idan wannan shine abin da zai dakatar da wannan abu, ina shirye in sauka, "inji shi.

Wednesday, January 2, 2019

ANKASHE MUTANE SHA TAKWAS 18, A KAUYUKKAN JIHAR ZAMFARA.

Ankashe mutane 18 akauykkan Jahar Zamfara
-----------------
Akalla mutane goma sha takwasne 18, aka ruwaito ankashe akayukkan karamar Hukumar Tsafe kauyen Dutsen Kure da kauyen Manasa kamar yadda jaridar Premium times ta ruwaito cewa maharan sun Mamaye Kauyukkan da safiyar Ranar Talata 01-01-2019.

Inda maharan suka kashe mutane tara 9 a kauyen Dutsen Kure da kuma kauyen Manasa sun kashe, kamar yadda premium times ta ruwaito mazauna kayukkan sunce Barayin sun Mamaye Garin saman Babura, da Bindigogi ahanayensu.

Maharan sun lalata dakunan ajiye abinci akauyukkan tareda lalata gidajen alummah wanda yanzu haka mazauna Garin sunyi kaura zuwa Jahar katsina. Kwamandan dake kula da yaki da hare hare yankin Shehu Mohammed, yace yanzu haka Yansanda nakokarin dawo da zaman lafiya yankin.


GWAMNATIN YARI BAZATA IYA GUDANAR DA ZABEN KANANAN HUKUMOMI BA.


Majalisar Dokokin a Zamfara ta kara waadain Shugabannin Kanan hukumomi 14, inda ta Tsige mataimakan Shugabannin 4 daga Mulki
-----------
Majalisar dokokin jahar Zamfara, yau laraba ta kara wa'adin Shugabannin kananan hukumomi goma sha hudu na jahar Zamfara, Wanda wa'adinsu ke karewa Yau 2 January 2019, wanda suka cika wa'adinsu na Shekara Ukku Kamar Yadda doka tayi tanadi. 

Majalisar takara masu wa'adi har zuwa ranar 2 April 2018, Haka kuma Majalisar dokokin ta Tsige wasu Shugabannin kanan hukumomi Ukku daga mukamansu wadanda suka hada da Mataimakan Shugabannin kananan hukumomin Zurmi, Birnin Magaji dana Gummi. 

Kamfanin dillacin Labaru na NAN, ya ruiwato cewa karin wa'adin ya biyo bayan rokonda Gwamnatin jahar Zamfara ta gabatar ga majalisa na neman a amince da karin wa'adin wanda kuma shugaban Majalisar Sanunsi Rikiji ya tabbatarda Karin waddin har nawata ukku wanda yace doka ta kananan hukumomi sakin layi na 15 karamin layi na hudu yabada damar karin waadin. 

Saidai wani danmajlisa mai wakiltar Maru ta Kudu, Hon. Abdullahi Muhammad Dansadau ya kalubalaci matakin tsige mataimakan shugabannin.

ANTSIGE MATAIMAKAN SHUWAGABANNIN KANANAN HUKUMOMI MULKI UKU A JIHAR ZAMFARA.

A yau ne wa'adin kananan hukumomi a jihar zamfara yake cika,  wanda aka masu na shekara uku kamar yadda doka ta tanada a jihar ya zamfara. Amma sai dai rashin samun aiwatar da zabe da ba'ayiba saboda dalilai na tsaro ya tilasta gwamnatin jihar neman majalisar dokokin jihar da ta  kara wa'adin wata uku ga shuwagabannin kananan hukumomin da kansilolan su.
Sai dai adai waje kuwa, majalisar dokokin jihar ta zamfara karkashin jagoranci Hon. Sanusi Garba Rikiji ta Ayyana wasu mataimakan kananan hukumomi guda uku wadanda Karin bai Shafa ba,  saboda basu biyayya ga gwamnatin Gwamna Abdul'aziz Yari.
Adai waje kuwa shima shugaban karamar hukumar Bukkuyum ya kwatanta irin wannan yunkuri ga wasu kansilolan Bukkuyum guda Hudu, inda yake tabbatar masu koda majalisar ta Kara wa'adin to sukam su San inda dare yamasu, don bazaiyi tafiya da suba tunda bakison gwamnatin Gwamna Abdul'aziz Yari Abubakar.

Daga

Aliyu Ahmad Gusau. 

Tuesday, January 1, 2019

GWAMNATIN ZAMFARA TA BADA KYAUTAR N8.5m GA IYALAN MARIGAYAN DA SUKA JI RAUNI.


Gwamnatin Zamfara ta ba da kyautar N8.5m ga iyalan marigayan da suka ji rauni.
Sojojin sun kai farmakin a lokacin da 'yan bindiga suka kai hari a lokacin da rundunar sojojin Najeriya da Nijar suka haɗu tare da su a Dumburum da ke yankin Zurmi Local Government of Zamfara.
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa wannan lamarin ya faru ne lokacin da masu aikata laifukan suka kaddamar da hare hare ga sojoji a lokacin da aka kashe mutane biyar a Nijar.
Gwamna AbdulAzeez Yari ya gabatar da kyautar ga Gwamnatin Jamhuriyar Nijar a ranar Litinin lokacin da ya ziyarci Maradi don yin sulhu tare da gwamnatin Nijar da kuma iyalan wadanda aka kashe.
Yari ya karbi ministan tsaron kasar Nijar, Kalla Muktari; Gwamna Maradi State, Zakiri Umar; da sauran jami'an gwamnatin Nijar.
Yari ya ce kyautar ita ce ta tallafa wa iyalan soja da aka kashe.

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTAR DA KANSA AKAN DAKATAR DA 'YAN MAJALISU HUDU DA AKAYI.

Daga Salisu Bello . Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar do...