Saturday, January 5, 2019

IDAN YARI BAI IYAWA, YA SAUKA_ INJI ATIKU

Dan Takarar shugaban Kasa a inuwar Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya soki kiran da gwamnan jihar Zamfara ya ke yi na a saka dokar ta baci a jihar saboda rashin tsaro da ake fama da shi.
Idan ba a manta ba ko a yau Alhamis gwamnan jihar Zamfara Yari ya bayyana wa manema labarai a fadar shugaban kasa cewa idan har saka dokar ta baci shine zai samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Zamfara a shirye yake da yayi murabus.
Sai dai kuma, kamar yadda yake ganin hakan ne kila mafita ga tsaron jihar, Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya fadi cewa sam basu tare a wannan shawara da yake badawa.
A takarda da Pharank Shuaibu ya fitar a madadin Atiku, ya ce wannan shiri ne kawai don a muzguna wa ‘Yan siyasa.
” Idan gwamnan jihar Yari ba zai iya ba kaucewa zai yi ya ba da wuri amma ba wai ya rika kira da a saka dokar ko ta baci a jihar ba. Yin haka sabawa doka ce da kuma muzguna wa mutane. Ana neman yadda za a takura wa mutane ne kawai a hana su walwala saboda son zuciya da kuma dagewa da Buhari yayi na sai dole-dole ya zarce ko da karfin tsiya ne.
Atiku ya kara da cewa muddun aka yi haka za a saka shingaye a tituna da wurare da dama a jihar da hakan zai takura wa walwalar mutane.

No comments:

Post a Comment

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTAR DA KANSA AKAN DAKATAR DA 'YAN MAJALISU HUDU DA AKAYI.

Daga Salisu Bello . Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar do...