Sunday, January 6, 2019

NAIRA MILIYAN 7 SUKA AMSA DON DAKATAR DA YAN MAJALISA HUDU (4).

Daga_
Abdulmuminu Sanusi.
Sanin kowane Mai bibiyar al'amuran siyasa ne Cewa, kwanakin nan jihar Zamfara ta fada cikin sabuwar dambarwar siyasa, Wadda har takai ga dakatar da 'yan majalisun Jihar su hudu wadan da ake zargi da laifukka da ba Suda tushe balle makama.

Bayan dogon bincike da jaridar Hantsi ta aiwatar mun gano ababen da aka nunke a cikin wannan badakalar ta dakatar da su.
Wani sashe na 'yan majalisun masu goyon Bayan gwamnatin sune Akaba zunzurutun Kudi har naira miliyan bakwai, ta hannun Mai tsawatar wa a majalisar Hon. Isah Abdulmuminu talatar Mafara.
Kuma Ko wane Dai daga cikin su, ya samu Naira Duhu Dari Uku da goma (310).
Duka wadannan ababe anyi sune sharar fage ga Kudirin dake akwai Kasa, na tsige mataimakin gwamnan Zamfara, Malam Ibrahim Wakkala Liman.
Saboda sunaso su Samar da Rinjaye Mai karfi a lokacin Gudanar da aikin tsige mataimakin gwamnan na Zamfara.
Allah ya kyauta.


1 comment:

  1. Aikin banza ai lokaci ya kure, dukan abunda gwamnatin jihar Zamfara zata yi a wannan lokacin bai kara Mata komai ga talakawan jihar Zamfara sai bakin jini da kyama domin Sun Riga sun bata rawar su da tsalle, Allah ya Isarwa Al'umar jihar Zamfara

    ReplyDelete

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTAR DA KANSA AKAN DAKATAR DA 'YAN MAJALISU HUDU DA AKAYI.

Daga Salisu Bello . Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar do...