Thursday, January 3, 2019

RAHOTON ZAMAN KOTU NA YAU ALHAMIS 3-1-2019


Daga... 
Ibrahim Bello Gusau Ibg

Abun da ake tsammani a zaman kotu na yau alhamis 3-1-2019 bai wuce na bayyanar shugabar hukumar zabe ta jahar zamfara, Dr. Asma'u Maikudi, ba amma hakan bai yuyu ba.

Jim kadan bayan shigowar mai shari'a, Justice Bello Muhammad Shinkafi, a zauren kotu, an fara gabatar da kai na lauyoyi daga kowane bangare kamar yadda aka al'adanta inda daga bisani anka gayyato dai daga cikin ma'aikatan wannan kotu mai suna Malam Bello da aka dora ma alhakin hannun ta sammace zuwa ga ita shugabar hukumar zabe ta jahar zamfara da yazo yayi ma kotu bayani inda aka kwana akan mika wannan sammace.

A cikin jawabin da yayi ma kotu, Malam Bello, ya bayyana cewa a lokacin da ya dauki wannan sammace zuwa ofishin ta, an hana shi ganin ta. Ya nemi sakatarin ta da ya hada shi da ita amma hakan bai yuyu ba.

Ya tambaye shi ina ta tafi, sai sakatarin yacce bai sani ba. Ya sake tambayar shi yaushe ake sa ran ta dawo, sai sakatarin yacce bai sani ba.

Ma'aikacin kotun, Malam Bello, ya dauki wannan sammace zuwa gidan ta domin hannun ta shi zuwa gare ta amma a cewar shi jami'an tsaron gidan na ta, sun ka hana shi ganin ta don haka wannan shi ne takaitaccen bayanin da zai yi ma kotu kuma yanzu haka ga sammacen a hannu shi.

SHARHI

Ga ka'ida ta kotu, idan irin haka ta faru, to abun da ake yi shi ne ; a lika sammacen a bakin ofishin wanda za a baiwa shi, ko a kofar gidan shi, ko kuma a buga shi a jarida sannan a ba da tsawon lokacin da ake sa ran zai ga sammacen. Idan kuma hakan ya chutura, sai kotu ta bada takardar izinin kamu  (Arrest Warrant) na a kamo shi a duk inda ya ke kuma idan haka ta faru, akwai dauri na tsawon wata shidda (6) a gidan yari.

-----------------------

Bayan da shi ma'aikacin wannan kotu ya kammala jawabi, sai lauyan Sanata Marafa, John shaka, ya miike tsaye inda ya gabatar da godiya da kuma yaba ma wannan kotu akan wadan nan matakan da ta dauka na ganin wannan sammace ya isa hannun Dr. Asama'u amma a cewar shi (Lauyan Marafa) la'akari da lokaci na ta tafiya, yana sanar da kotu cewa ya janye wannan bukatar ta gayyato ita wannan shugabar hukumar ta zabe kuma zai tsaya daga nan.

A dayan bangaren, lauyan uwar jam'iyyar APC ta kasa ya nemi kotu da ta ba shi dama domin gabatar da wasu takardu da ake sa ran martani ne (Counter Claim) ga wata bukata da lauyan Sanata Marafa ya shigar a kwanakkin baya inda shi lauyan Sanata Marafa yayi gyara da shari'ar shi cewa yana rokon kotu cewa idan ta hukunta cewa ba a yi zabe ba, a lokaci daya yana neman kotu da ta umurci uwar jam'iyyar APC da ta shirya sabon zaben fidda gwani a cikin kwana bakwai (7) kachal, wanda wannan gyaran ne lauyan bangaren uwar jam'iyya ke son maida martani (Counter claim) inda wannan bukatar ta shi (lauyan uwar jam'iyya) ta hadu da turjiya daga lauyan Sanata Marafa da kuma lauyan bangaren ma su shigar da kara (gwamnati) wanda daga nan ne mai shari'a ya dage zaman kotun inda anka je hotu har sai an dawo.

Bayan dawowa daga hutu na farko da na biyu, mai shari'a, Justice Bello Muhammad Shinkafi, ya aminta da waccan bukatar da lauyan bangaren uwar jam'iyya ya gabatar inda anka ba shi nan da zuwa gobe jumu'a 4-1-2019 da ya gabatar da abun da yake so ya gabatar.

Domin kauce ma cigaba da kawo rudani a cikin al'umma, lauyan Sanata Marafa, John shaka, ya nemi kotun da ta hana kowane irin lauya yin hira da yan jaridu bayan zaman kotu har sai an kammala shari'ar baki dayan ta domin a cewar shi, suna kawo rudani a cikin al'umma a dalilin irin bayanan da su ke baiwa yan jaridu kuma kotu ta aminta da hakan.

Daga karshe, an dage zaman kotun har sai zuwa gobe jumu'a 4-1-2018 idan mai rayuwa da kashewa ya kaimu.

Allah ya ci gaba da dora ma su gaskiya akan makaryata a kotu.


No comments:

Post a Comment

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTAR DA KANSA AKAN DAKATAR DA 'YAN MAJALISU HUDU DA AKAYI.

Daga Salisu Bello . Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar do...