Friday, January 4, 2019

'YAN MAJALISAR JIHAR ZAMFARA, SHIN KO GWAMNA A A YARI YA GYARA NE?


Maganar gaskiya jihar zamfara muna da yan majalisun jaha da basusan me ya kamata ba. Na saurari jagoran majalisar dokoki ta jahar Zamfara yana cewa, "Duk da yake Munje hutu kuma ba zamu dawo bakin aiki ba sai 15 ga watan Janairu na wannan shekara, mun Kira zaman gaugawa ne domin la'akari da muhimmancin da ke akwai ga bukatar da Gwamna ya ya gabatar mu na, ta karin Wa'adin watanni hudu ga shuwagabannin kananan hukumomi na jaha."

Abun ban haushi da takaici anan shine, duk kashe-kashen nan da akeyi a fadin jahar zamfara, ba suga muhinmancin janye hutunsu su dawo domin janyo hankalin gwamnati da tayi abunda ya dace domin tsare rayukan al'ummar da suke wakilta ba, amma suna iya dawowa akan matsalar ciyamoma.

Wallahi! Al'ummar Zamfara mudawo cikin hayyacin mu zabi wakillai na gari ba irin wadannan jeka na yika  ba, wadanda suka dauki samun su da rashin su suka ta'alla kashi ga wani  mai mulki.

Ku dubi yadda a jihar Zamfara yadda gwamna ya wulakanta majalisa, ya maidasu tamkar wani bangare na majalisar zartawwa.

Shi kakakin majalisar Sunusi Rikiji ya zamto tamkar jeka na yika, bayan Al'ummar mazabar Gusau ta daya suka tura shi don wakilce su, ya maida Gwamna tamkar wani dodo, duk da shi ne ya taba fada a kafofin yada labarai na gida da na waje cewa " gwamna Abdul'aziz yari ya cika dukkan sharuddan tsigewa daga karagar mulki".
Shin abin tambaya a nan, Shi Gwamnan ya gyara ne, don al'ummar Zamfara na cikin duhu, saboda maganar tabi shanun talla.

Yan majalisar jahar Zamfara sun watsar da damar da kundin tsarin mulki ya basu, sun jefa al'ummar jahar Zamfara cikin halin kunci, domin sun kasa aiwatar da ayukkan da Al'umma suka zabo su domin aiwatar ma su!

Wai kamar yadda ma su iya magana kance,: "Kukan kurciya jawabi ne amma fa ga mai hankali".

No comments:

Post a Comment

GWAMNAN JIHAR ZAMFARA YA NISANTAR DA KANSA AKAN DAKATAR DA 'YAN MAJALISU HUDU DA AKAYI.

Daga Salisu Bello . Gwamnan Jihar Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar ya nisantar da kan sa da sa hannu wajen dakatar da 'yan Majalisar do...